in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
CIIE ya samar da karin damammaki ga kasashe masu tasowa
2018-11-10 16:16:13 cri

"Zo mana, zo mana, ku dandana ruwan zuma daga dajin Zambia", "Ku zo ku ji dadin shan ice-cream irin na Turkiyya, wanda aka yi da kayan lambu"……A yankin baje kolin kayayyakin abinci, da amfanin gona da aka kaddamar a bikin CIIE, 'yan kasuwa daga kasashe masu tasowa sun yi namijin kokarin gabatar da kayayyakin abinci, da amfanin gona na kasashensu, sun kuma ja hankulan dimbin 'yan kasuwa domin neman yin shawarwari da su.

"Budewar fure kadai ba ya alamtar zuwan lokacin Bazara, ana tabbatar da zuwa lokacin Bazara ne kadai idan furanni daban daban suka bude". Wannan wata tsohuwar waka ce ta al'ummar Sinawa, dake bayyana fatan yin hadin gwiwa, a lokacin da ake kokarin yin wani abu. Shugaban kasar Sin ya kan yi irin wannan kira a wasu tarukan kasa da kasa. A yanzu abun da yake so ke nan ya tabbata a yayin bikin CIIE. A lokacin da kasashe masu arziki suke nune-nunen fasahohin zamani irin nasu, da kayayyakin dake da kunshe da fasahohin zamani, kasashe masu tasowa, da kuma kasashe wadanda har yanzu suke fama da kangin talauci, sun zo da kayayyakin dake bayyana halayen musamman nasu, kamar kayayyakin abinci, da amfanin gona, da tufafi, da kayayyakin masarufi, da kayayyakin yawon shakatawa, da kuma kayayyakin tarihi na nuna abubuwan da bil Adama ke ta'ammali da su, inda suka yi gogayya da na kasashe masu arziki a dandali guda. A yayin bikin, an san cewa, al'ummomin kasashe daban daban, dukkansu suna da 'yancin jin dadin zamansu, kuma bai kamata a bar kowa a baya, a kan hanyar neman samun ci gaba ba. Tunanin "kafa al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama" da shugaba Xi Jinping ya gabatar a da, da ra'ayinsa na "tsayawa matsayin yin hakuri, da kuma cin moriyar juna, domin ciyar da kasashe daban daban gaba tare" wanda shugaban ya gabatar a cikin jawabin da ya yi a yayin taron kaddamar da CIIE, dukkansu sun nuna mana wata hanyar da za a iya bi, domin cimma burinmu.

A hakika dai, wannan biki na CIIE, ya zama wani misali game da yadda ake bin tunanin yin hakuri da juna, a lokacin da ake neman ci gaba. Yawan kamfanoni da masana'antu da suka halarci baje kolin ya kai fiye da 3600, sannan yawan kasashe da yankuna, da kuma kungiyoyin kasa da kasa da suka halarci bikin ya kai 172, ciki har da kasashe mambobin kungiyar G20, da na kungiyar BRICS, da na SCO, da kuma kasashen da shawarar bunkasa "ziri daya da hanya daya" ta shafa, da kasashe 35 wadanda har yanzu ke fama da kangin talauci.

Wannan ya alamta cewa, wadanda suka halarci bikin sun fito daga dukkanin fadin duniya. A waje daya, hukumar shirya baje kolin CIIE ta samar da rumfuna biyu kyauta ga kowace kasa wadda ke fama da kangin talauci.

Bisa kokarin kasar Sin da sauran kasashen duniya, wannan baje koli na CIIE, ya kasance kamar wani lambun shan iska, inda dukkan kasashen duniya suke cin moriya sakamakon bunkasar tattalin arzikin duniya bai daya.

Bisa rahoton da MDD ta fitar a watan Yulin bara, game da halin da kasashe masu fama da kangin talauci suke ciki, har yanzu, yawan kasashen da har yanzu suke fama da kangin talauci ya kai fiye da 40, kana yawan jarin da kasar Sin ta zuba a wadannan kasashe shi ne mafi yawa. A yayin taron kolin kungiyar BRICS da aka shirya a birnin Johnnesberg na kasar Afirka ta kudu a watan Yulin bana, shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, "Kasar Sin wadda za ta samu ci gaba sosai a nan gaba, kasa ce mai tasowa har abada. Tabbas za mu tsaya tsayin daka, wajen goyon bayan sauran kasashe masu tasowa." Wannan baje koli na CIIE ya bayyana cewa, yanzu kasar Sin na cika alkawarin da ta dauka.

Yanzu haka, wasu kasashe na yunkurin nuna adawa da bunkasa tattalin arzikin duniya bai daya, har ma suna yunkurin ba da kariya ga cinikayyarsu. Sakamakon haka, ana fuskantar matsin lambar raguwar saurin bunkasar tattalin arzikin kasa da kasa. Tattalin arzikin kasashe masu tasowa, da na kasashe masu fama da kangin talauci, sun fi samun barazana saboda tattalin arzikinsu dake kan karshen zango na masana'antun samar da kayayyaki.

Idan ana son cimma burin da ake da shi a ajandar samun dawaumammen ci gaba nan da shekarar 2030 ta MDD, domin tinkarar hadurra, da kalubalolin da bil Adama ke fuskanta, bai kamata a dogaro kan kasar Sin kadai ba, dole ne dukkan kasashen duniya sun yi hakuri da bambancin al'adu, da ra'ayoyin dake kasancewa tsakaninsu, ta yadda za su iya bayar da gudumamwar su cikin hadin gwiwa, domin neman ci gaba tare.

A cikin jawabin da ya bayar a yayin kaddamar da wannan biki na baje kolin CIIE, shugaba Xi Jinping ya nuna cewa, "a lokacin da ake bunkasa tattalin arzikin duniya bai daya a yau, idan mai karfi zai zazzagi maras karfi, ko duk wanda ya ci nasara zai ci riba shi daya, za su kasance kamar wani titin da ba za a iya fita daga cikin sa ba. Yin hakuri da juna domin neman cin moriya da kuma nasara tare, shi ne zai kasance kamar wani titin da za a iya samun makoma mai haske a kan sa." Sakamakon haka, za a iya fadin cewa, wannan biki na CIIE, ya bude wata sabuwar kofa ga wadanda suke neman hanyar gaskiya, a lokacin da suke neman samun ci gaba. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China