Babbar jami'ar zartaswar kamfanin Nyumbani Coffee, da ta halarci baje kolin, Fridah Mbaya, ta ce ta ji dadin zuwa Shanghai don halartar bikin CIIE, inda ta ce ya gabatar da kayayyakinta ga babbar kasuwa, musammam tsanakin al'ummar Sinawa.
Shi kuwa Koos Balaauw, daga kasar Namibia, ya CIIE a matsayin wanda ya samarwa 'yan kasuwa dandalin hadin gwiwa, don kamfanonin kasar Sin su zuba jari a kasashen Afrika, haka zalika su ma kamfanonin nahiyar, wanda ya ce na da nufin kara bunkasa kasashen ta hanyar kulla kawance don samun damar fitar da kayyaykinsu.
Cikin wani sakon email da ya aikewa kamfanin dillancin labarai na Xinhua, Keith Rock, draktan sashen yada labarai da hulda da jama'a na hukumar kula da cinikayya ta duniya WTO, ya ce bikin ya bayyana bukatar hadin gwiwa da kulla kawance a harkar cinikkayya tsakanin kasa da kasa, musammam kasar Sin da nahiyar Afrika. (Fa'iza Mustapha)