in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Syria tana aiki tukuru don kawo karshen yakin basasar kasar
2018-10-30 13:26:29 cri
Ministan harkokin wajen kasar Syria Walid al-Muallem ya sanar a jiya Litinin cewa gwamnatin Sham tana yin aiki tukuru domin lalibo hanyar siyasa da nufin kawo karshen yakin basasar da kasar ta tsunduma cikinsa sama da shekaru 7 da suka gabata, kamfanin dillancin labaran kasar SANA shine ya bada rahoton.

Al-Muallem yace, gwamnatin Syriar ta riga ta amince da shiga duk wata tattaunawar kasa da kasa wanda zata haifar da kyakkywan sakamakon warware takaddamar kasar, na baya bayan nan shine batun goyon bayan yunkurin kafa kwamitin shirya kundin tsarin mulkin kasar.

Ministan yayi wannan tsokaci ne a lokacin ganawarsa da wakilan shugabannin kwamitin wanzar da zaman lafiya na kasa da kasa da kungiyar matasa ta kasa da kasa mai rajin kafa demokaradiyya wadanda suka yi ganawar a birnin Damascus na kasar Syriar.

Sai dai ya nanata cewa, batun amfani da hanyoyin siyasa don warware rikicin kasar Syriar baya bukatar yin katsalandan daga kasashen ketare, musamman ma kan batun da ya shafi shirya dokokin tsarin mulkin kasar.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China