Shugaban ma'aikatan firaministan kasar Fitsum Arega, ya bayyana yayin wani taron manema labarai a jiya cewa, tsarin bada visa bayan isa kasar ga 'yan Afrika masu ziyara, ya yi daidai da burin Firaministan kasar Abiy Ahmed na tabbatar da dunkulewar nahiyar.
Habasha na fatan shirin zai taimaka wajen saukaka dunkulewar tattalin arzikin nahiyar Afrika ta hanyar kara ingantawa da bunkasa harkokin yawon bude ido.
Kasar ta gabashin Afrika da ta kasance mazauni ga hedkwatar Tarayyar Afrika AU, na fatan yunkurin zai taimakawa shirin AU na tabbatar da zirga-zirga jama'a ba tare da shinge ba. AU ta bukaci dukkan kasashen Afrika su rika bada bisa bayan isa kasar ya zuwa shekarar 2023. (Fa'iza Mustapha)