in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hadarin jirgin kasa ya hallaka mutane 18 a lardin Taiwan
2018-10-22 09:47:13 cri
Jiya Lahadi da yamma, jami'an gwamnatin gundumar Yilan ta lardin Taiwan na kasar Sin sun bayyana cewa, wani jirgin kasa na Puyuma mai lamba 6432 ya yi hadari, inda ya kauce daga kan layinsa, a lokacin da yake ratsawa ta tashar Xinma dake gundumar, al'amarin da ya hallaka mutane 18, tare da jikkatar wasu 164, ciki har da mutane 171 wadanda aka riga aka tantance su. Bisa labarin da muka samu daga hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa ta Taiwan, an ce, daga cikin mutanen da suka mutu ko suka ji rauni, guda 1 ne dan asalin Amurka, yayin da sauran fasinjojin mutanen wurin ne.

An ce, dukkan tarago takwas na jirgin kasan sun kauce daga kan layi, ciki har da gudu hudu wadanda suka kife. Gaba daya fasinjoji 366 ne a cikin jirgin, kuma tuni aka garzaya da wadanda suka ji rauni zuwa asibiti. A halin yanzu ana nan ana gudanar da binciken musabbabin aukuwar hadarin.

Wannan shi ne hadarin jirgin kasa mafi muni da ya auku a cikin shekaru 37 da suka gabata a lardin na Taiwan.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China