Babban manajan kamfanin watsa labarai na Zanzibar na Tanzaniya Muhammed Seif Khatib, ya bayyana a yau Jumma'a a nan birnin Beijing cewa, ingantar hadin-gwiwar kafofin watsa labaran Sin da Afirka, na taimakawa sosai ga ci gaban dangantakarsu.
A wajen taron majalisar zartarwa karo na uku, na kungiyar hadin-gwiwar kafofin watsa labaran talabijin na Afirka, wato "Africa Link Union" a turance, Muhammed Seif Khatib ya ce, kamfaninsa na yin hadin-gwiwa tare da kamfanin CCTV+, da kamfanin dillancin labaran kasar Sin wato Xinhua, wajen yin musanyar bidiyo, da labarai, da kuma rahotanni, tare kuma da tura ma'aikatansa kasar Sin don su samu horo. (Murtala Zhang)