Hukumomin kasar Sin, sun kara kai kaimi wajen karfafawa bangarori masu zaman kansu shiga harkokin zuba jari a fannin samar da kayayyakin more rayuwa domin karfafa tattalin arzikin kasar.
Ayyukan da suka shafi kayayyakin more rayuwa sun hada da na makamashi da sufuri da manyan tituna da ma'ajiyar adana ruwa da wuraren kawar da shara.
A karshen shekarar 2017, kasuwancin bangarori masu zaman kansu ne ya mamaye sama da kaso 60 na alkaluman GDP na kasar Sin, kuma sun samar da ayyuka sama da kaso 80 a birane. (Fa'iza Mustapha)