in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun tsaron tekun Libya sun ceto bakin haure 116 a gabar tekun yammacin kasar
2018-09-26 10:52:19 cri

Sojojin ruwa masu tsaron tekun Libya a jiya Talata sun samu nasarar ceton 'yan cirani 116 a gabar tekun yammacin kasar.

Dakarun tsaron sun gudanar da aikin ceton ne a tekun mai tazarar kilomita 50 daga birnin Zuwara, wanda ke da nisan kilomita 120 daga babban birnin kasar Tripoli, inji Ayob Qassem, kakakin sojojin ruwan kasar.

An gudanar da aikin ceton ne karkashin hadin gwiwar dakarun tsaron teku da masu kula da tankokin mai, kafin daga bisani aka kwashe bakin hauren zuwa wata cibiyar da aka tsugunar da su.

Ko a ranar Litinin ma, dakarun tsaron tekun Libyan sun ceto bakin haure 235 a ayyukan sintiri da suka gudanar.

Libya ta kasance a matsayin wata matattarar da bakin haure ke amfani da ita wajen tsallakawa ta tekun Bahar Rum zuwa kasashen Turai sakamakon karuwar tashin hankali da matsalar tsaro a kasar ta arewacin Afrika tun bayan kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Libyan marigayi Muammar Gaddafi a shekarar 2011. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China