in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Karfafa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka zai tallafawa kasashen Afirka, in ji masaniyar Masar
2018-09-13 11:20:20 cri

 

Daga ranar 3 zuwa ranar 4 ga wata, aka cimma nasarar gudanar da taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka wato FOCAC a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Taron da ya janyo hankulan masanan kasa da kasa. A nata bangare, shugabar sashen Sinanci na jami'ar Alkahira na kasar Masar, kana shugabar kwalejin, Rehab Mahmoud ta yaba matuka da shirye-shiryen "Manyan matakai takwas" da kuma "Karfafa dunkulewar Sin da Afirka cikin hadin gwiwa" da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, inda take ganin cewa, karfafa hadin gwiwar dake tsakani Sin da Afirka zai taimakawa kasar Masar, har ma da dukkanin kasashen Afirka baki daya.

Yanzu ga karin bayani da Maryam Yang ta hada mana:

Yayin da take hira da wakilin CRI, malama Rehab Mahmoud ta bayyana cewa, shirin "Manyan matakai takwas" na hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka da shugaba Xi Jinping ya gabatar, ya burge ta kwarai da gaske. Tana mai cewa, "Shugaba Xi Jinping ya yi cikakken bayani kan wannan shiri na "Manyan matakai takwas", da kuma yadda za a aiwatar da shirin, cikin jawabin da ya yi yayin taron FOCAC, lamarin da ya burge ni sosai. Kasar Sin da kasar Masar kasashe ne masu tasowa, kuma halayen mutane da yanayin zaman takewar al'ummar kasar Sin da kasashen Afirka suna kama a wasu bangarori, tabbas wadannan matakai takwas za su ba da taimako matuka ga kasar Masar, da ma sauran kasashen Afirka baki daya a fannoni daban daban."

Karfafa dukulewar kasar Sin da kasashen Afirka cikin hadin gwiwa shi ne babban taken taron FOCAC na birnin Beijing, shugaba Xi Jinping ya gabatar da jerin matakai cikin jawabin da ya gabatar a yayin taron, domin karfafa dukulewar Sin da Afirka yadda ya kamata. Malama Rehab ta kuma yabawa shirin "kara dunkulewar Sin da Afirka bisa fannin jin dadin zaman rayuwa", inda aka mai da hankali kan karfafa hadin gwiwar Sin da Afirka wajen kyautata zaman rayuwar al'umma. Ban da haka kuma, ta bayyana ra'ayinta kan shirin "kara dukulewar Sin da Afirka a fannin raya al'adun Sin da Afirka". Ta ce, "Kara dukulewar Sin da Afirka a fannin raya al'adu yana nufin habaka mu'amalar dake tsakanin wakilan Sin da Afirka a fannonin al'adu, fasahohi, ba da ilmi, motsa jiki, 'yan mata da matasa da dai sauransu. Lamarin da ya nuna cewa, ban da taimakawa kasashen Afirka ta hanyar zuba jari, Sin tana mai da hankali kan musayar al'adu dake tsakaninta da kasashen Afirka. A ganina al'adu na da muhimmanci kwarai. Ta hanyar kara sanin al'adun wata kasa, za mu iya kara saninmu kan halayen mutane da kuma yanayin zaman takewar al'ummar wata kasa, shi ya sa, al'adu zai iya karfafa sanin juna da fahimtar juna a tsakanin Sin da Afirka, ta yadda za a iya habaka hadin gwiwa da mu'amalar dake tsakanin bangarorin biyu yadda ya kamata."

Dangane da zargin da wasu kasashen yammacin duniya suka yi kan hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, cewar Sin tana gudanar da "sabon mullkin mallaka" da kuma kwashe albarkatun kasashen Afirka, malama Rehab ta nuna kiyayyarta kan wannan zargin. Tana mai bayyana cewa, "Ban amince da wannan ra'ayi ba ko kadan, ya kamata ko wace kasa ta nemi ci gaban kanta. Haka kuma, shugaba Xi Jinping ya ce, kasar Sin ta nuna girmamawa da goyon baya da kuma adalci ga kasashen Afirka a yayin da take hadin gwiwa da su. Wannan ita ce hanyar da kasar Sin take bi a kokarin habaka hadin gwiwar dake tsakaninta da kasashen Afirka. Na yi imanin cewa, tabbas kasar Sin za ta hada kai tare da kasasahen Afirka wajen neman hanyoyin ci gaba da za su dace da halayen da kasashen suke ciki, kuma wannan ba ra'ayi na ba ne ni kadai, ra'ayi ne na al'ummomin kasashen Afirka."

A sa'i daya kuma, malama Rehab ta ce, galibin kafofin yada labarai na kasashen Afirka sun yabawa taron kolin FOCAC na wannan karo da aka yi a birnin Beijing na kasar Sin, kana, al'ummomin kasashen Afirka suna ci gaba da kara fahimtarsu kan kasar Sin bisa ci gaban hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka.

Haka zalika, shekarar bana shekara ce ta cika shekaru 40 da kasar Sin ta bude kofa ga waje, malama Rehab ta ce, fasahohin kasar Sin wajen aiwatar da wannan shiri na bude kofa ga waje za su kasance abin koyi ga kasar Masar, har ma da dukkanin kasashen Afirka baki daya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China