in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bayani kan shahararriyar 'yar wasan kwallo kafar kasar Najeriya-Asisat Oshoala
2018-09-13 10:12:54 cri


1. Za mu fara ne kuma da bayyana kadan daga tarihin wannan 'yar wasan kwallon kafa

An haifi Asisat Lamina Oshoala a ranar 9 ga watan Oktoban shekarar 1994, a Ikorodu dake jihar Legas ta tarayyar Najeriya. Tana da tsayin mita 1.78, sa'an nan 'yar wasan gaba ce. Yanzu haka tana taka kwallo ne a kulob din Dalian Quanjian F.C. dake birnin Dalian na kasar Sin. Wanda ya kasance wani kulob mai karfi cikin tsarin wasan kuloflika mafiya karfi a kasar Sin wato Chinese Women's Super League.

Lambobin karramawa da Asisat Oshoala ta taba samu sun hada da lakabin 'yar wasa mafi kwarewa, da wadda ta fi samun maki a gasar cin kofin duniya ta 'yan mata matasa wato FIFA U-20 Women's World Cup ta shekarar 2014. Ban da haka duk a shekara 2014, ita Asisat da abokan kungiyarta ta Super Falcons, wato kungiyar mata ta wasan kwallon kafa ta Najeriya, inda suka cimma nasarar samun kambi a gasar cin kofin Afirka ta mata. Asisat ta zama 'yar wasa mafi kwarewa, gami da ta biyu mafi cin kwallo. Kaza lika ma iya cewa, ita daya ce daga cikin 'yan wasan kwallon kafa mata mafiya kwarewa a nahiyar Afirka, ganin yadda ta taba zama Miss Football din nahiyar Afirka har sau 3. A shekarun 2014, 2016, gami da 2017.

2. Yayin da ake bayani kan wani dan wasan kwallon kafa, ko kuma wata 'yar wasa, a kan raba bayanin zuwa gidaje 2, wato game da wasannin da ta buga a cikin kulob dinta, gami da sauran wasannin da ta shiga a cikin kungiyar kasarta. To, a nan za mu bayyana nasarorin da Asisat ta samu a cikin kuloflikan da ta bugawa kwallo.

Ta fara aiki a matsayin kwararriyar 'yar wasan kwallon kafa a shekarar 2009, wato lokacin da take da shekaru 15 da haihuwa, inda ta halarci kulob din FC Robo Queens dake Lagos, Najeriya, a matsayin wata 'yar wasa matashiya. Wanna kulob ya shahara a kasar Najeriya, har ma a daukacin nahiyar Afirka, ganin yadda ya tattara shahararrun 'yan wasa mata dake taka leda a kulob din, wadanda suka hada da ita Asisat, da Esther Sunday, da Rashidat Ajibade, da Aminat Yakubu, da dai sauransu. Asisat tana taka leda a wannan kulob har zuwa shekarar 2013, lokacin da take da shekaru 19 a duniya. Sa'an nan ta sauya sheka zuwa kulob din Rivers Angels, dake Port Harcourt, jihar Rivers ta kasar Najeriya, wanda shi ma ya kasance daya daga cikin kuloflika mafi karfi a kasar.

Bayan ta yi shekaru 2 tana taka leda a Rivers Angels, a ranar 23 ga watan Jainairun shekarar 2015, Asisat Oshoala ta halarci kulob din Liverpool Ladies na kasar Birtaniya. A lokacin manajan kulob din Liverpool Matt Beard ya yabi Asisat, inda ya ce ita " daya ce daga cikin 'yan wasa matasa mafi kwarewa a duniya".A lokacin duk da cewa akwai jita-jitar da aka yada cewa tana da niyyar shiga wani kulob ta daban, amma a karshe ta shiga Liverpool, kuma tana farin cikin taka leda a can. A madadin kulob din Liverpool, Asisat ta taka leda a wasanni 9 cikin tsarin Premiur league, inda ta jefa kwallaye 3 cikin raga. Sai dai ba ta samu gama wasannin kakar wasa ta 2015 ba, domin raunin da ta samu a gwiwarta ya sa dole ta huta har tsawon watanni 2. Wannan ma ka iya haifar da tasiri ga kulob dinta, ganin yadda kulob din na ta ya kasa kare kambin da ya samu a baya, har ma ya zama na bakwai a cikin dukkan kuloflika 8 da suka halarci gasar Premiur league. Daga bisani, a watan Janairun shekarar 2016, kulob din Liverpool ya sanar da shirin Asisat na sauya sheka zuwa kulob din Arsenal Ladies dake birnin London. Bayan da Asisat ta shiga Arsenal a 2016, ta bugawa kulab din wasanni 11, inda ta buga kwallaye 2 cikin raga, har ma ta taimakawa kulob din zama na farko a tsarin Premiur League na mata na kasar Birtaniya.

Sai dai bayan da ta kammala ayyukanta a kakar wasan 2016, ta sake sauya sheka zuwa wani kulob dake kasar Sin.

A ranar 10 ga watan Fabrairun shekarar 2017, kulob din Dalian Quanjian F.C. ya kulla yarjejeniya da Asisat. Bayan da ta zo kasar Sin, Asisata ta taka rawar gani, inda a kakar wasa ta 2017, ta samu buga kwallaye 12 cikin raga a wasannin tsarin gasar Super League na kuloflika mafi karfi na kasar Sin, ta yadda ta taimakawa kulob dinta kare kambinsa a tsarin gasar. Ita kanta ma ta samu wasu lambobi yabo daga masu kula da tsarin gasar. Daga bisani duk a shekarar 2017, Asisat ta taimakawa Dalian Quanjian samun nasarar lashe gasar Super cup, wadda ita ce gasar da take gudana tsakanin zakarun manyan tsare-tsaren gasanni guda 2 na kasar Sin. Ban da wannan kuma, a wajen bikin bayar da lambobin karammawa na hukumar wasan kwallon kafa ta nahiyar Afirka na shekarar 2017, Asisat ta zama Miss Football, wato 'yar wasa da ta fi taka rawar gani a wancan kakar wasa tsakanin dukkan 'yan wasan mata na nahiyar Afirka.

Dimbin nasarorin da Asisat ta samu a kakar wasa ta 2017 sun sa kuloflikan Liverpool da Arsenal sun nuna niyyar dawo da ita cikin kungiyoyinsu, sai dai a wannan karo Asisat ba ta amsa gayyata da kuloflikan suka yi mata ba, inda ta ce za ta ci gaba da taka kwallo a kasar ta Sin. Kuma tana sa ran samun karin ci gaba a kakar wata ta 2018.Ban da haka ta kara da cewa, a lokacin da ta bar Arsenal don komawa kasar Sin, mutane da yawa sun nuna shakku kan matakin da ta dauka, sai dai ta gayawa kanta za ta iya. Sa'an nan nasarorin da ta samu a shekarar 2017 sun shaida cewa, kundurin da ta tsayar daidai ne.

3. Sa'an nan a bangaren taka kwallo a kungiyar kasar Najeriya, Asisat ta fara samun nasara sosai a lokacin da take taka leda a matsayin 'yar wasan gaba cikin kungiyar Najeriya ta matasa. Sa'an nan bayan da ta shiga kungiyar kasa ta baligai, ta taka leda a matsayin 'yar wasan dake tsakiya. Bisa lakabin da abokan wasan ta suka ba ta, za mu iya ganin kwarewarta. Lakabin da ya hada da "Seedorf", wato sunan shahararren dan wasan kasar Netherland Clarence Seedorf, da kuma "Superzee".

Tauraronta ya fi haskakawa tsakanin shekarun 2014 da 2016, inda Asisat ta taimakawa kungiyar Najeriya Super Falcons wajen lashe gasar zakarun kuloflika a nahiyar Afirka karo 2, a 2014, da kuma 2016. Irin gudunmowar da ta baiwa kungiyar kasarta, ta sa a watan Satumban shekarar 2014, shugaban kasar Najeriya a lokacin Goodluck Jonathan, ya ba ta babbar lambar kyautar "Member of the Order of the Niger" MON, lambar da a kan baiwa mutumin da ya samar da babbar gudunmowa ga Najeriya.

Sauran lambobin kyauta da ta taba samu sun hada da

Queen of The Pitch Award: 2014

African Women's Youth Player of the Year: 2014

African Women's Championship Golden Ball: 2014

FIFA U-20 Women's World Cup Golden Boot: 2014

FIFA U-20 Women's World Cup Golden Ball: 2014

BBC Women's Footballer of the Year: 2015[18]

Aiteo CAF Best Player Award 2017(Female Category)

Chinese Women's Super League Top scorer: 2017

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China