in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta dakatar kociyan Super Eagles bisa zargin rashawa
2018-09-13 16:22:35 cri

Hukumar kula da kwallon kafan Najeriya ta tabbatar a jiya Laraba cewa ta dakatar da kociyan babbar kungiyar wasan kwallon kafan kasar Salisu Yusuf bisa zarginsa da hannu na aikata rashawa.

Yusuf, wanda aka haramtawa dukkan harkokin da suka shafi wasannin kwallon kafa har na tsawon shekara guda ba tare da bata lokaci ba, kana an umarceshi da ya biya tarar dala dubu 5 ga hukumar wasan kwallon kafa ta Najeriyar cikin watanni uku.

Hukumar gudanarwar wasan kwallon kafan kasar tace kociyan ya gaza amsa tambayoyin da aka yi masa bayan da aka bashi damar kare kansa bisa zargin da ake yi masa.

Yusuf, wanda ya kasance mutumin dake da matukar farin jini a fagen wasannin kwallon kafan Najeriya, har yanzu baice uffan game da dakatarwar da aka yi masa ba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China