in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jam'an diflomasiyyar kasashen Afrika sun jadadda muhimmancin dake tattare da dangantakar nahiyar da kasar Sin
2018-09-08 16:24:38 cri
Wasu jami'an diflomasiyya na kasashen Afrika, sun jadadda muhimmanci dake tattare da dangantakar nahiyarsu da kasar Sin, su na masu bayyana zumidin ganin ta kara karfi a nan gaba.

Jakadan Gabon a Amurka Micheal Moussa-Adamo, ya shaidawa mahalarta wani taron liyafa a gidansa cewa, shigar kasar Sin nahiyar Afrika, ya haifar da ginin dimbin ababen more rayuwa tare da inganta rayuwar jama'a da kuma samar da moriyar juna tsakanin bangarorin biyu.

An gudanar da taron ne domin murnar nasarar kammala taron koli na dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika wato FOCAC, wanda aka kammala ranar Talata da ta gabata a nan birnin Beijing.

Jakadu da masu fada a ji daga kasashen Afrika sama da 30 ne suka halarci liyafar.

Da yake jawabi ga taron, Jakadan Jamhuriyar Congo a Amurka kuma wani mashiryin taron, Serge Mombouli, ya ce yadda shugabannin kasashen Afrika 53 ko kuma wakilansu suka halarci taron na Beijing a bana, ya nuna yakini da jajircewar nahiyar Afrika na kara zurfafa huldarta da kasar Sin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China