A yayin ganawar, shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, Sin ta nuna goyon baya da taimakawa kasar Afirka ta Tsakiya wajen shimfida zaman lafiya da raya kasa, Sin tana son kara yin imani da juna a fannin siyasa tare da kasar Afirka ta Tsakiya, da fadada hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, da taimakawa kasar a fannin samar da abinci da inganta rayuwar jama'a, za kuma ta ci gaba da tura tawagar likitoci zuwa kasar Afirka ta Tsakiya.
A nasa bangare, Touadera ya bayyana cewa, kasarsa tana godiya ga kasar Sin bisa ga taimakon da take ba ta wajen samar da zaman lafiya da ci gaban kasar, kana tana son kara yin mu'amala a tsakanin jam'iyyun kasashen biyu da kuma manufofin raya kasa, da hada kai wajen zurfafa dangantakar dake tsakaninsu, da kara yin hadin gwiwa bisa shawarar "ziri daya da hanya daya" da manyan ayyuka 8 da shugaba Xi Jinping ya gabatar a yayin taron kolin FOCAC na wanna karo da aka kammala a birnin Beijing. (Zainab)