A halin yanzu, kasashen Afirka suna dukufa wajen neman ci gaba da kansu, yayin da kuma ake raya ayyukan masana'antu da neman ci gaba. Bangarori daban daban na kasashen Afirka, na sa ran taron FOCAC na wannan karo, zai iya inganta shirin "Ziri daya da hanya daya", domin ba da taimako gare su wajen neman bunkasuwa, yayin da ake habaka hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka.
Yara suna wasa a karkashin babbar gada da motoci ke bi a jihar Neja ta kasar Nijeriya.
Wani jirgin kasa na lantarki da aka kera bisa ma'aunin kasar Sin, yana tafiya kan layin dogo a jihar Kaduna na kasar Nijeriya.
Ma'aikata mazauna wurin, wadanda aka yi ayyukan gina layin dogo a birnin Abuja na kasar Nijeriya tare da su.