A hanlin yanzu dai, Sin na jawo hankalin jarin ketare sosai duk da irin takadammar ciniki da halin tattalin arziki duniya mai cike da sarkakiya, mene ne dalili? Akwai su uku:
Na farko: Sin ta kan yi kokarin kyautatawa da daga matsayin halin shigo da jari da kawar shingaye.
Na biyu: Sin ita kadai na da wani rinjaye ta fuskar jerin sana'o'i da karfin samar da kayayyaki da rinjayen da take da shi a fannin kasuwanni, matakin da ya goyi bayan kamfanoni masu jarin ketare.
Na uku: Sin na da niyyar ci gaba da matakin bude kofa ga kasashen waje.