in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kafofin watsa labaran Amurka na maida hankali kan shawarwarin da za'a yi tsakanin Sin da Amurka kan harkokin tattalin arziki da kasuwanci
2018-08-20 11:24:29 cri
A karshen watan nan, za'a gudanar da shawarwari tsakanin manyan jami'an gwamnatocin Sin da Amurka kan batutuwan tattalin arziki da kasuwanci a birnin Washington na kasar Amurka, al'amarin da ya jawo hankalin kafofin watsa labaran kasar sosai.

Rahotannin wasu kafofin watsa labaran Amurka da dama sun ruwaito cewa, sake farfado da shawarwari tsakanin kasashen biyu ta fuskar tattalin arziki da kasuwanci zai karfafawa kasuwanni gwiwa. Wata kafar watsa labarai ta talabijin mai suna CNBC a Amurka ta bada rahoton cewa, a ranar 17 ga wata, matsakaicin alkaluman hada-hadar hannayen jari na Dow Jones ya karu da maki 110.59, wanda ya kai maki 25669.32 a karshe.

Har wa yau, akwai wasu kafofin watsa labaran Amurka wadanda suka bayyana damuwar jama'ar kan manufofin gwamnatin kasar. Rahoto daga jaridar Washington Post ya ce, masana tattalin arzikin Amurka da dama sun soki gwamnatin kasar saboda kara sanya haraji kan kayayyakin da take shigarwa da su daga kasar Sin, hakan a cewarsu, zai haifar da ja-in-ja tsakanin kasashen biyu ta fannin tattalin arziki da kasuwanci. Bugu da kari, a wani labari na daban da kafar talabijin ta CNBC ta ruwaito, an yi nazarin cewa, kara sanyawa kayayyakin Sin haraji ka iya kawo tsaiko ga farfadowar tattalin arzikin Amurka.

Tuni a ranar 16 ga wata, ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta sanar da cewa, bisa goron gayyatar da Amurka ta ba ta, mataimakin ministan kasuwanci na kasar Sin, kana mataimakin wakilin kasar Sin na yin shawarwari kan kasuwancin kasa da kasa, Wang Shouwen zai kai ziyara Amurka a karshen watan nan, inda zai tattauna da takwaransa na Amurka David Malpass.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China