in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shawarar Ziri Daya da Hanya Daya za ta taimakawa rage talauci a Afirka
2018-08-16 14:10:47 cri


A ranar Talata, an kaddamar da taron rage talauci da ci gaba, karkashin laimar dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka na FOCAC na shekarar 2018 a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. A wajen taron dake gudanar a birnin Beijing, jami'ai na kasar Sin da na kasashen Afirka, sun yi nazari kan taken taron na "shawarar Ziri Daya da Hanya Daya da hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka ta fuskar rage talauci", inda suka tattauna hanyoyin da za a iya bi don sanya gwamnatoci, da kamfanoni, da masana, da kungiyoyin kasa da kasa da na al'umma su shiga a dama da su, a kokarin aiwatar da shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, gami da gudanar da hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka a fannin kau da talauci.

Liu Yongfu, darektan ofishin kau da talauci karkashin majalisar gudanarwar kasar Sin, ya yi jawabi a wajen taron, inda ya ce kasar Sin da kasashen Afirka suna bin hanya daya a kokarin neman raya kansu, kana kau da talauci da neman samun ci gaba mai dorewa, buri ne na bai daya ga daukacin al'ummar Sin da ta kasashen Afirka. Saboda haka, ya kamata bangarorin Sin da Afirka su kara musayar ra'ayi, da kafa wani tsarin hadin gwiwa na aikin rage talauci karkashin laimar shawarar Ziri Daya da Hanya Daya. Ya ce, "Cikin shekaru 5 da suka wuce, ana ta kokarin aiwatar da shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, lamarin da ya shafi kasashe da kungiyoyin kasa da kasa fiye da 100, ciki har da wasu kasashen dake nahiyar Afirka. Bisa kaddamar da wasu ayyuka na hadin gwiwa, da kafa wata yanar gizo ta kayayyakin more rayuwa, da habaka hadin gwiwar da ake yi a fannin masana'antu, da kara kokarin daidaita manufofin kasashe daban daban, jama'ar kasa da kasa sun samu alfanu sosai. Cikin shekarun 5, yawan kudin cinikin da aka yi tsakanin Sin da wadannan kasashe ya zarce dalar Amurka biliyan 5000. Yayin da kasar Sin ta zuba jarin da ya kai dalar Amurka biliyan 70 ga kasashen, tare da samar musu da guraben aikin yi dubu 200. Wannan ya shaida cewa, shawarar Ziri Daya da Hanya Daya na taimakawa raya tattalin arziki, da rage talauci, gami da baiwa kasashe daban daban damar samun ci gaba tare."

Zuwa yanzu, kasashen Afirka da suka kulla yarjejeniya da kasar Sin don nuna niyyarsu ta halartar shawarar Ziri Daya da Hanya Daya sun hada da Afirka ta Kudu, da Senegal, da Rwanda, da kuma Mauritius. A nasa bangaren, Marie Cheong, minista mai kula da hadin kan al'umma da raya tattalin arziki na kasar Mauritius, wanda shi ma yake halartar taron, ya gaya wa wakilin CRI cewa, "Kasar Sin ta samu ci gaba mai ban mamaki a fannin rage talauci. A shekarun baya bayan nan, kasar tana fatar da jama'a kimanin miliyan 10 daga kangin talauci a kowace shekara, haka kuma tana da shirin kau da talauci kaco kan nan da shekarar 2020. Saboda haka kasar na tare da dimbin fasahohi na ci gaba, wadanda za su iya taimakawa nahiyar Afirka a fannin rage talauci. Ya kamata kasashen Afirka su shiga a dama da su a shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, domin kasar Sin za ta samar da fasahohi, da kudi, da kayayyaki, gami da wasu kwararrun ma'aikata. Haka zalika, kasar Sin za ta mika wa sauran kasashen wadannan fasahohi, tana kuma son hadin gwiwa da su, da taimaka musu wajen rage talauci. "

Ban da haka, Josefa Sacko, kwamishina mai kula da tattalin arziki a kauyuka da aikin gona na kungiyar tarayyar Afirka ta AU, ta jaddada cewa, kasashen Afirka na son kara yin hadin gwiwa da kasar Sin a fannin raya aikin gona, da tattalin arzikin kauyuka, don taimakawa rage talauci da raya tattalin arziki a kasashen Afirka, ta ce "Bisa hadin gwiwar da ake yi tsakanin kungiyar AU da kasar Sin, bangarorin 2 sun yi musayar fasahohi, da tura wa juna tawagogin kwararru. Mun samu goyon baya daga bangaren kasar Sin ne, a fannonin dasa bishiyoyi, da kau da kwari, da sarrafa amfanin gona, da dai sauransu."

Wannan taro na kau da talauci da neman ci gaba, shi ne irinsa na 8 da aka taba gudanarwa, wanda ya kasance wani reshen dandali ne ga dandalin FOCAC. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China