A cewar mai magana da yawun shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta kudu Khuselu Diko, kasashen biyu suna da tarihi na dadadden hadin gwiwa mai karfi bisa manyan tsare-tsare, inda ya ba da misali da alakar kasashen a bangaren kwamitin sulhun MDD da sauran harkokin da suka shafi tattalin arziki. Haka kuma kasashen sun daga matsayin alakarsu zuwa dangantakar manyan tsare-tsare, daya daga cikin alakar diflomasiya mafi girma.
Wani mai sharhi kan harkokin siyasar kasar Afirka ta kudu Somadoda Fikena na ganin cewa, ziyarar shugaba Xi a Afirka ta kudu za ta kara zurfafa alakar Sin da Afirka ta kudu, kasancewarsu mambobin BRICS baya ga alakar dake tsakaninsu a siyasance.
Ziyarar ta Xi dai wani bangaren ne na kara kyautata alakar siyasa da tattalin arziki , da jin dadin jama'a da ma hadin gwiwa a harkokin kasa da kasa tsakanin sassan biyu, kamar yadda fadar shugaban kasar Afirta ta kudun ta wallafa a shafinta na Twitter. (Ibrahim Yaya)