Jakadan na Sin ya bayyana hakan ne, a jawabin sa yayin bude taron mahawarar kwamitin tsaron MDD game da yanayin da gabas ta tsakiya ke ciki.
Ma ya jaddada goyon bayan kasar Sin game da kafuwar kasar Falasdinu mai cikakken 'yanci dake da hedkwata a gabashin birnin Kudus, kamar yadda hakan ke kunshe cikin tsarin shata kan iyaka na shekarar 1967.
Jakadan na Sin ya ce domin shawo kan matsalar gabas ta tsakiya, Sin a shirye take ta yi aiki da kasashen shiyyar da lamarin ya shafa, domin lalubo hanyoyin magance kalubalen da ake fama da shi. (Saminu)