Birnin Chishui dake arewacin lardin Guizhou, muhimmin wuri ne mai manyan bishiyoyi da aka dasa a mafarin kogin Yangtse, yawan bishiyoyin da aka dasa ya kai kashi 82.85 cikin dari, wanda ya ke na farko a lardin Guizhou, kana wanda ke kan gaba a dukkan fadin kasar Sin. Yayin da ake kokarin dawo da yankin bishiyoyi da a baya a kasance yankunan gonaki, an kuma fara shuka gora a wannan yanki, ta yadda za a raya sha'anin gora yadda ya kamata. A shekarar 2017, an yi nasarar kawar da talauci a wannan wuri. (Zainab)