in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ranar yaki da kuma hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta duniya
2018-07-05 18:44:42 cri

Majalisar dinkin duniya ce ta kebe ranar 26 ga watan Yunin kowace shekara a matsayin ranar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta duniya, domin ilimantar da jama'a game da illar da miyagun kwayoyi ke haddasawa a cikin al'umma.

Wannan rana ta samu goyon bayan daidaikun jama'a da daukacin al'umma da sauran kungiyoyi a dukkan fadin duniya. A hannu guda kuma, ofishin MDD mai yaki da miyagun kwayoyi da manyan laifuffuka (UNODC) ya tsara shirye-shiryen Ilimantar da jama'a game da yaki da wannan matsala daga dukkan fannoni.

Ofishin na UNODC ya kuma bayyana cewa, kusan mutane miliyan 200 ne ke ta'ammali da miyagun kwayoyi, wadanda suka hada da hodar Iblis. Wannan ya sa MDD ta kebe wannan rana domin kawar da wannan matsala da ta addabin duniya.

Masu fashin baki na cewa, galibi matasa ne ke shiga wannan matsala, sakamakon rashin aikin yi ko tasirin abokai, ko rashin tarbiya da sauransu. Don haka, akwai bukatar iyaye da sauran masu ruwa da tsaki su dukufa wajen ilimantar da musamman matasa illar shan miyagun kwayoyi, ta yadda za su kasance masu amfanawa kansu da ma al'umma baki daya.

Bugu da kari, kamata ya yi mahukunta a dukkan matakai, su gindaya tsaurara ka'idoji game da yadda za a rika sayar da wasu nau'o'in magunguna ga jama'a, don hana shagunan sayar da magunguna, sayarwa mutane wasu magunguna dake iya yin illa ga lafiyar bil-Adama ba tare da iznin likita ba. Masu iya magana na cewa, idan kunne ya ji, to gangan jiki ya tsira. (Saminu, Ibrahim/Sanisu Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China