Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Gao Feng ya bayyana a yau 21 ga wata cewa, Sin da Amurka sun samun ci gaba mai armashi kan shawarwari ta fuskar cinikayya, amma Amurka ta yi amai kuma na lashe. Mr. Gao Feng ya furta hakan ne yayin wani taron manema labarai da aka yi a wannan rana game da lamarin cinikayyar Sin da Amurka.
Gao ya jaddada cewa, idan Amurka ta fitar da takardar kara kakabawa kasar Sin karin haraji, wadda ta sabawa dokar cinikayyar kasa da kasa, za kuma ta haddasa rashin adalci, Sin ta shirya tsaf don mayar da martani, kuma tana tsayawa tsayin daka wajen kiyaye moriyar jama'arta. Ya kuma nanata cewa, Sin za ta iya tinkarar duk wani sauya matsayin da Amurka ta aiwatar a nan gaba.(Amina Xu)