Kakakin ma'aikatar harkokin kasuwanci na kasar Sin ya yi jawabi kan sanarwar da fadar shugaban kasar Amurka ta fitar a jiya, inda ya ce, Amurka ta yi barazanar fitar da takardar kakaba karin haraji kan kayakin kasar Sin da darajarsu ta kai dala biliyan 200, bayan takardar da ta riga ta fitar a baya-bayan nan, na kakaba haraji kan kayakin kasar Sin da darajarsu ta dala biliyan 50, wanda mataki ne na rashin imani da watsi da ra'ayin bai daya da bangarorin biyu suka cimma cikin shawarwarinsu, al'amarin da kasashen duniya ke bakin ciki sosai da shi. Ya ce Idan Amurka ta ci gaba da nuna halin rashin imani da gabatar da wannan takarda, Sin za ta mayar da martani mai karfi.
Kakakin ya nuna cewa, yadda Amurka ta tada yakin cinikayya ya sabawa ka'idojin kasuwaci, kuma bai dace da moriyar kasashen duniya ba, wanda kuma ke barazana ga moriyar kasashen biyu da ta jama'arsu, har ma ya kai ga lalata moriyar jama'ar duniya. Matakin da Sin ta dauka na kiyaye moriyar kasar da jama'arta, ya kasance matakin kare tsarin ciniki cikin 'yanci da moriyar bil Adam bai daya. (Amina)