Hukumar binciken sararin samaniya ta kasar Sin CNSA ce ta bayyana hakan a Alhamis din nan. Tauraron dan Adam din dai shi ne irin sa na farko a fannin ayyukan sadarwa da ke aiki a wannan falaki, zai kuma aza harsashin aikin da ake sa ran na'urar Chang'e-4 za ta gudanar, na'urar da ake fatan ita ce za ta kasancewa irin ta ta farko, da za ta sauka a wannan bangare na duniyar wata.
Da yake karin haske game da hakan, shugaban kwalejin nazarin ayyukan fasahohin sama jannati na kasar Sin Zhang Hongtai, ya ce yayin da tauraron ke sararin samaniya, zai iya hangen duniyar bil Adama, da kuma sashe mafi nisa na duniyar wata.