in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sannu a hankali tawagar Super Eagles za ta goge, in ji Koci Rohr
2018-06-04 09:29:44 cri
Mai horas da tawagar kwallon kafar Najeriya Gernot Rohr, ya ce tawagar Super Eagles ta yanzu, za ta bunkasa sannu a hankali, kasancewar a wannan lokaci tana kunshe ne da 'yan wasa wadanda matsakaitan shekarun su ba su wuce 24 ba.

Kocin Rohr ya bayyana hakan ne, yayin zantawar sa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a 'yan kwanakin da suka gabata. Ya ce a ganin sa karan tawagar zai kai tsaiko ne nan da shekarar 2022 lokacin da za a buga gasar cin kofin duniya ta gaba. Don haka ya dace masu goyon bayan kungiyar su lura da halin da ake ciki, gabanin fara buga gasar cin kofin duniya ta bana da za a bude nan da 'yan kwanaki a Rasha.

Rohr mai shekaru 64 a duniya, ya kara da cewa, burin sa shi ne horas da 'yan wasan na Super Eagles zuwa ga cimma gagarumar nasara a nan gaba, kasancewar ya amince ya tsawaita kwantiragin sa da kungiyar har zuwa shekarar 2020. Ya ce nan da 'yan shekaru masu zuwa za a cimma burin ganin tawagar Najeriya mai cikakken karfi, da kwarewar lashe wasanni yadda ya kamata.

Kocin wanda a baya ya bugawa kungiyoyin Bayern Munich, da Girondins Bordeaux wasa, ya ce yana farin ciki da goyon bayan da ake nunawa kungiyar ta Najeriya, to sai dai fa akwai bukatar kallon al'amarin ta mahangar da ta dace, duba da cewa kungiyar za ta buga wasa a gasar ta cin kofin duniya a rukunin D mai kungiyoyi dake da gogewa, wanda ya kunshi kasashen Argentina, da Croatia da Iceland. Rohr ya ce sai sa'ar gaske kungiyar za ta ma iya fita daga wannan rukuni.

A ranar 11 ga watan nan da muke ciki ne dai tawagar ta Super Eagles za ta tashi zuwa Rasha, bayan atisayen da ta yi a sansanonin ta dake Najeriya da Austria. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China