Wakiliyar musammam ta shirin yara a yankunan rikici na MDD, Virginia Gamba, ta ce ta samu kwarin gwiwa daga sakin yara 210 ciki har da 'yan mata 3, da 'yan tawayen bangarori masu rikici da juna suka yi a ranar Juma'ar da ta gabata.
Cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya, Virginia Gamba, ta alakanta sakamakon da aka samu da dorewar kiraye-kirayen MDD da al'ummomin kasashen waje.
Ta ce sakin yaran 210 da aka yi a ranar Juma'a, ya kawo adadin yara da aka saki tun farkon wannan shekara zuwa 800.
An saki yaran ne daga kungiyar adawa ta SPLM-IO da kuma ta NSF, a ranar Juma'ar da gabata a yankin Pibor dake gabashin Sudan ta kudu. (Fa'iza Mustapha)