Donald Kaberuka wanda ya bayyana haka a jiya, yayin da yake zantawa da Xinhua, a gefen taron gidauniyar Mo Ibrahim dake gudana a birnin Kigalin Rwanda, ya ce ya kamata gwamnatocin Afrika su rungumi shirin sosai, domin yankin na nufin ci gaba ga al'ummar nahiyar.
Ya kara da cewa, za a ga yadda cinikayya tsakanin kasashen Afrika zai bunkasa cikin saurin da ba a taba gani ba.
Ya ce abun da ya rage kawai shi ne, rattaba hannu a hukumace domin tabbatar da shi, inda ya ce ya yi imanin cewa, galibin kasashen nahiyar za su rattaba hannu a kai.
Masanin kan harkokin tattalin arziki, ya ce nahiyar za ta magance matsalar shingen cinikayya da ake fuskanta bayan an rattaba hannu kan shirin.
Har ila yau, ya ce yankin ciniki mara shinge zai bada gagagrumar gudunmuwa ga dorewar ci gaban tattalin arziki da rage fatara da samar da aikin yi da kuma dunkulewar nahiyar Afrika.
Yankin ciniki cikin yanci na nahiyar Afrika, na da nufin samar da kasuwa guda ta nahiyar ga hajoji da hidimomi da hada-hadar kasuwanci da zuba jari ba tare da wani shinge ba. A cewar Tarayyar Afrika, wannan zai ba da dama gaggauta kafa kungiyar kasashen nahiyar da ta Tarayyar, wadda za ta amince da kudin haraji na bai daya. (Fa'iza Mustapha)