in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da hukumar hadin gwiwa da samun bunkasuwa ta kasa da kasa ta kasar Sin
2018-04-19 19:55:24 cri
A kwanan nan ne aka kaddamar da hukumar hadin gwiwa da samun bunkasuwa ta kasa da kasa ta kasar Sin. Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana a yau 19 ga wata a nan birnin Beijing cewa, Sin za ta ci gaba da bin ra'ayin samun moriya mai dacewa, da nuna imani da juna, da rage gibin dake tsakanin kasashe masu ci gaba da masu tasowa, da kuma sa kaimi ga neman makoma irin ta bai daya ga bil Adama.

A gun taron manema labaru da aka gudanar a wannan rana, madam Hua ta yi nuni da cewa, kafa hukumar hadin gwiwa, da samun bunkasuwa ta kasa da kasa ta kasar Sin, muhimmin kuduri ne da aka tsaida bisa jigon shugabancin Xi Jinping. Kana muhimmin mataki ne na kiyaye zaman lafiya a duniya da samun bunkasuwa, kuma yana da babbar ma'ana a fannin inganta tsarin harkokin diplomasiyya, da hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu bin shawarar "ziri daya da hanya daya". (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China