Babban daraktan hukumar zuba jari ta kasar Tanzaniya TIC, Geoffrey Mwambe, ya bayyana cewa suna gayyatar masu zuba jari daga kasar Sin domin su zuba jarinsu a Tanzaniyan, inda ya bayyana cewa, a shirye suke su ba su dukkan taimakon da suke bukata.
TIC hukuma ce ta gwamnatin kasar Tanzaniya wanda ke gudanar da aikin karfafa gwiwa da bunkasa harkokin zuba jari a kasar da kuma baiwa gwamnatin kasar ta Tanzaniya shawarwari game da dukkan batutuwan da suka shafi zuba jari.
Mwambe ya bayyana cewa, mu'amalar cinikayya tsakanin kasar Tanzaniya da kasar Sin yana ci gaba da gudana cikin kyakkyawan yanayi, inda ya bayyana cewa kasar Sin ta kasance babbar abokiyar cinikayyar kasar Tanzaniya ce, ya zuwa shekarar 2016, yawan jarin ciniki tsakanin kasashen biyu ya kai dalar Amurka biliyan 3.88.
Jami'in hukumar ta TIC ya ce, kasar Sin ta kasance kasa ta biyu mafi samar da jarin kasashen waje wato FDI ga kasar Tanzaniya, kuma akwai kamfanonin kasar Sin kimanin 724 da suka yi rajista da hukumar ta TIC, kana akwai wasu 'yan kasuwar kasar Tanzaniya masu yawa dake ci gaba da kulla yarjejeniyar ciniki da takwarorinsu na kasar Sin.
Ya ce dangantaka a tsakanin kasashen biyu ta kasance muhimmiya idan aka yi la'akari da irin muhimman ayyukan da kamfanonin kasar Sin suke gudanarwa a kasar, ko kuma irin taimakon da gwamnatin kasar Sin take bayarwa wajen aiwatar da ayyuka a Tanzaniyan.
Mwambe ya ce, ana gayyatar masu zuba jarin kasar Sin domin su zuba jari a fannonin masana'antu, aikin gona, kiwon dabbobi, kiwon kifi, ma'adanai, yawon bude ido, da gina kayayyakin more rayuwa da fannin fasahar sadarwa ta zamani.(Ahmad Fagam)