in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Niyyar Trump a bayyane take!
2018-04-11 21:16:44 cri
Jiya Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi a wajen taron shekara-shekara na dandalin tattaunawa na kasashen Asiya da ya gudana a garin Boao, inda ya gabatar da wasu muhimman matakai hudu na kara bude kofar kasarsa ga kasashen waje, abun da ya samu babban yabo da goyon-baya daga kasashen duniya.

Game da wannan batu, shugaba Donald Trump ya wallafa wani sako a shafinsa na Twitter, inda ya ce ya godewa shugaba Xi Jinping sosai saboda kalamansa na abuta, kan batun harajin kwastan, da batun shigar da motoci kasar, har ma Trump ya godewa Xi Jinping saboda manufofinsa a fannonin da suka shafi ikon mallakar fasahohi, da kuma batun musanyar fasahohi. Trump ya kuma ce shugabannin biyu za su yi kokari don samun karin ci gaba tare.

Yayin da ake takaddamar cinikayya tsakanin Sin da Amurka, Trump ya wallafa irin wannan sako, wanda ya nuna kamar zai yi sassauci kan matsayar sa da shugaba Xi. Dalilan hakan kuwa sun hada da,

Na farko, Trump na fuskantar babban matsin lamba daga kasashe daban-daban, don haka ba yadda zai yi illa kawai ya bayyana wannan furuci.

Bayan da shugaba Xi Jinping ya gabatar da jawabi a dandalin Boao, kafofin yada labaran kasashen yammacin duniya suna ganin cewa, matakan fadada bude kofar kasarsa ga kasashen waje da Xi Jinping ya sanar, sun bayyana irin niyyar kasar Sin ta fannin kiyaye dunkulewar dukkanin fadin duniya baki daya. Jaridar NewYork Times ta wallafa bayanin dake cewa, jawabin Xi Jinping, da kalaman Trump na tada fitina sun bambanta sosai. Shi ma kamfanin dillancin labarai na AP ya ce, shugaba Xi Jinping na kokarin ganin cewa kasarsa wato Sin za ta iya kare harkokin cinikayya da hadin-gwiwa na duniya, amma shi Donald Trump na kokarin kawo tsaiko ga harkokin shigar da hajoji kasarsa.

Na biyu, duk da cewa Trump ya ce ya godewa Xi Jinping, amma ainihin niyyarsa ita ce, gurgunta fahimtar kasashen duniya.

A cikin sakonsa a shafin Twitter, Trump ya ce ya godewa kasar Sin kan matakan kara bude kofa ga kasashen ketare, amma wannan ba ita ce ainihin niyyarsa ba, Abun da Trump ke so shi ne, ya gurgunta fahimtar kasashen duniya a kan cewa, wai kasar Sin na da niyyar yin sassauci da Amurka. Wato Trump na son kara samun amincewa daga kasashe daban-daban a cikin takaddamar cinikinta da Sin.

Gaskiyar magana ita ce, gwamnatin Trump ba ta yi hangen-nesa ba, ta kuma gaza fahimtar manyan tsare-tsare gami da hangen-nesan da gwamnatin kasar Sin ta yi. Da duk wanda ya san tarihin kasar Sin na aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, za ku iya fahimtar cewa, a cikin shekaru arba'in da suka shige, kasar Sin ta dunga aiwatar da manufar bisa hakikanin halin da ake ciki, kuma ta hanyar da ta dace. Shugaba Xi Jinping ya sanar da wadannan sabbin matakai na fadada bude kofa ga kasashen waje, amma sam ba domin maida martani ga Amurka yayin takaddamar ciniki ba ne, illa kawai matakai ne wadanda tun tuni gwamnatin kasa Sin ta tsara.

Dalili na uku shi ne, Donald Trump na son kwantar da hankalin bangarori daban-daban a kasarsa wato Amurka.

Abun da ya kamata gwamnatin Trump ya ba fifiko shi ne, tabbatar da matsayin jam'iyyar Republican a Amurka, da kwantar da hankalin al'ummar kasar. Tun da Amurka ta tada rigimar cinikayya da kasar Sin, gwamnatin Trump ta sha suka daga sanatoci, da kungiyoyin masu mallakar sana'o'i daban-daban, da masu mallakar kamfanoni da kafafen watsa labarai da dai sauransu.

A halin yanzu, Trump na son kwantar da hankalin jama'ar kasarsa. A daidai wannan lokaci ne kuma, ya ce wai ya godewa Xi Jinping saboda jawabin da ya gabatar a Boao, wanda dai ba shi ne nufin sa ba, illa dai yana fatan isarwa al'ummar Amurka wani sako dake nuwa cewa, wai matakansa suna da amfani, har sun sa kasar Sin ta ja da baya.

Amma al'ummar Amurka ba za su yarda da hakan ba. Inda wata kafar yada labaran Amurka ta nuna cewa, Trump bai yi tunani sosai ba a wajen kaddamar da takaddamar ciniki da kasar Sin, wanda hakan ya sa ake kara nuna damuwa kan makomar Amurka a nan gaba.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China