Da take tsokaci game da hakan, shugabar hukumar zartaswar AU kuma ministar harkokin wajen kasar Rwanda Louise Mushikiwabo, ta ce ya kamata kasashen nahiyar su lura da cewa su ne za su tabbatar da yadda yankin ciniki cikin 'yanci na nahiyar zai kasance. Ta na mai cewa dukkanin kasashen nahiyar na da rawar takawa don ganin an cimma nasara.
Ministar wadda ke wannan tsokaci a birnin Kigalin kasar Rwanda, ta ce ya zama wajibi kasashen Afirka, su tunkari kalubalen dake gaban su, wanda suka hada da na dokoki, da na samar da kudade daga sassa masu zaman kan su, da na ababen more rayuwa, da batun ayyukan lura da shige da fice, muddin dai suna fatan ganin ci gaba a fannin bunkasar cinikayya tsakanin su.