Vera Songwe, wadda ke bayyana hakan yau Litinin a birnin Kigalin kasar Rwanda, ta ce ana ci gaba da samun shingaye ga kasuwanni a sassan duniya daban daban, matakin da ka iya shafar Afirka, amma manufar AfCFTA ta zamo wani ginshiki na daidaita tsarin Afirka, don shiga a dama da ita a hada hadar cinikayya a yankin da take, tare da share mata fagen samun ci gaba mai dorewa.
Jami'ar ta kara da cewa, Afirka na da damar samun bunkasa, idan har kasashen nahiyar suka yi hadin gwiwa, maimakon daukar matakai na daidaikun kasashe. A cewar ta, yayin da ake fuskantar hali na rashin tabbas a kasuwannin duniya, ya dace nahiyar Afirka ta hada kai wajen duba irin na ta damammakin cimma nasara na bai daya.