A lokacin gudanar da taron kolin na AU game da batun tsarin na AfCFTA, wanda aka bude shi a jiya Asabar a Kigalin kasar Rwanda, da dama daga cikin jakadun sun bayyana cewa kasashensu sun amince zasu rungumi tsarin na AfCFTA.
A cewar kungiyar ta AU, ana saran shugabannin kasashen na Afrika zasu rattaba hannu kan yarjejeniyar kafa tsarin na ciniki marar shinge wato AfCFTA, wadda ake son kaddamar da shi a ranar 21 ga watan nan na Maris, kana itace ranar karshe ta kammala taron kolin.
Evariste Koffi Yapi, zaunannen wakilin kasar Cote d'Ivoire a kungiyar ta AU yace, Afrika tana da dubun damammaki na kasuwanci wanda zata samarwa miliyoyin al'ummarta, sai dai nahiyar ta gaza aiwatar da matakan da zasu samar da wadannan damammakin da take dasu sakamakon karancin damammakin ciniki a tsakanin kasashen nahiyar.
A cewar Gairy M. Saddigh, zaunannen wakilin kasar Libya a kungiyar ta AU, kafa tsarin na AfCFTA, zai bada gagarumar gudunmowa wajen bude kofar damammakin cinikayya a tsakanin kasashen nahiyar, wanda zai yi matukar bunkasa harkokin shigar da kayayyaki da fitar dasu ketare a tsakanin shiyyoyin nahiyar.
Tsarin na AfCFTA zai samar da kasuwanni masu tarin yawa na hada-hadar hajoji a tsakanin kasashen na Afrika, matakin da zai habaka tattalin arziki da kawo sauye-sauye da kyakkyawar makoma, kana zai taimaka wajen bunkasa cigaban masana'antun nahiyar ta Afrika, inji Ndumiso Ntshinga, zaunannen wakilin Afrika ta kudu a AU.