Hukumar koli ta bin bahasin jama'ar kasar Sin ta gabatarwa majalisar NPC rahoton aiki
A yau Jumma'a ne, shugaban hukumar koli ta bin bahasin jama'a ta kasar Sin Cao Jianming ya gabatar da rahoton hukumar a yayin taron farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin wato NPC karo na 13, inda ya gabatar da ayyukan da hukumar ta gudanar a shekaru 5 da suka gabata a fannoni 7, tare da yanayin yin bincike da magance laifufukan da aka aikata a yayin da jami'an suke gudanar da ayyukansu. Mr. Cao ya bayyana cewa, a cikin shekaru 5 da suka gabata, hukumomin dake bin bahasi na kasar Sin sun gudanar da bincike kan mutane fiye da dubu 250 da ake zargin su da aikata laifufuka a yayin da suke gudanar da ayyukansu, inda ake rage hasarar da yawansu ya kai Yuan fiye da biliyan 55 da miliyan 300. Kana hukumar ta hada gwiwa tare da sauran hukumomin kasar, inda aka yi nasarar tiso-keyar masu aikata laifufuka 222 daga kasashe da yankuna 42 da suke samun mafaka. (Zainab)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku