Mr. Ghassan Salame, ya yi wannan kira ne yayin wani taro da tawagar wakilan al'ummar Zawiyah, birni mai nisan kilomita 45 daga Tripoli fadar mulkin kasar ta Libya, taron da ya gudana a hedkwatar tawagar MDD mai aikin wanzar da zaman lafiya a kasar ko UNSMIL a takaice.
Jami'in ya ce ya kamata a gudanar da aikin rajistar masu kada kuri'a, da kuma kammala dokokin gudanar da kuri'un jin ra'ayin jama'a gabanin aiwatar da hakan.
A nasu bangaren, wakilai daga garin na Zawiyah sun gabatar da wasu batutuwa masu muhimmanci, wadanda za su taimaka wajen cimma daidaito, tare da kawo karshen rabuwar kai a fannin siyasar kasa. (Saminu)