in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kudurin taron AU game da kawar da cin hanci a kasashen nahiyar
2018-02-11 14:18:11 cri

A Litinin 29 ga watan Janairin shekarar 2018 ne, aka rufe taron kolin kungiyar tarayyar Afirka wato AU karo na talatin a birnin Addis Ababan kasar Habasha. A yayin taron, an tattauna kan batutuwan da suka jibinci yaki da cin hanci da karbar rashawa da murkushe ayyukan ta'addanci, da dunkulewar tattalin arzikin nahiyar waje guda.

Manazarta na ganin cewa, Afirka na samun bunkasa a 'yan shekarun nan, amma duk da haka tana fuskantar wasu manyan kalubaloli, don haka akwai bukatar shugabannin kasashen nahiyar su hada kai don daukar matakan raya nahiyar.

Alkaluma na nuna cewa, sama da rabin al'ummar Afirka na ganin cewa, gwamnatocin kasashen nahiyar sun kasa kawar da matsalar cin hanci da rashawa yadda ya kamata, inda matsalar ta yi babbar illa ga ci gaban rayuwar al'umma.

Kungiyar Transparency International mai fafutukar yaki da cin hanci da rashawa ta duniya ta fitar da alkaluman dake cewa, daga shekara ta 2014 zuwa 2015, akwai 'yan Afirka kimanin miliyan 75 wadanda aka tilasta su aikata cin hanci, dalilin da ya sa akwai 'yan Afirka da dama dake ganin cewa, matsalar cin hanci na dada kamari a nahiyar.

Yarjejeniyar yaki da cin hanci da rashawa da AU ta zartas a shekara ta 2003 ta shaida irin kudirin kasashen Afirka na yakar matsalar. Amma har zuwa yanzu, ba'a kai ga warware matsalar yadda ya kamata ba, har ma tana kara yin illa ga ci gaban tattalin arzikin Afirka, da kawo nakasu ga matakan tsaro a nahiyar.

Baya ga matsalar cin hanci da rashawa, matsalar ta'addanci a nahiyar Afirka wani muhimmin batu ne na daban da aka tattauna a gun taron. Babu tantama, akwai sauran rina a kaba game da murkushe ayyukan ta'addanci a nahiyar ta Afirka.

Masana na ganin cewa, yaki da ayyukan ta'addanci, ba ma kawai yana bukatar daukar matakan soja ba, yana kuma bukatar daukar matakan siyasa da na tattalin arziki. Sannan dole ne a kara sanin dalilan dake haddasa bullar ta'addanci, da daukar matakai a fannonin da suka shafi habaka tattalin arziki da rage kangin talauci da jama'a ke fuskanta.

Har wa yau, babbar matsala ta uku da ta dabaibaye nahiyar Afirka ita ce, rashin mu'amala mai karfi ta fannin kasuwanci tsakanin kasashe membobin kungiyar ta AU. Domin karfafa alakar tattalin arziki da kasuwanci tsakanin kasashen Afirka, kungiyar tarayyar Afirka ta dade tana kokarin kafa wani yankin ciniki maras shinge a nahiyar.

Wani batu da kasashen nahiyar ke fatan cimmawa shi ne, kafa yankin cinikayya maras shinge a watan Yunin shekara ta 2015 matakin ake ganin, zai taimaka wajen rage tsaiko da harajin kwastam ke kawo wa harkokin kasuwanci tsakanin kasashe daban-daban na nahiyar, da samar da damammaki da alfanu ga kamfanoni gami da masu sayayya, ta yadda Afirka za ta samu ci gaba

Rahotannin da kungiyar AU ta fitar a baya, sun nuna cewa, kusan kowace kasar Afirka na da nata tsari na sa ido kan harkokin kwastan, kana, akwai bambanci sosai tsakanin kasashen Afirka a fannonin da suka shafi bude kofa ga kasashen waje da ra'ayin kafa yankin cinikayya maras shinge.

Masu sharhi na cewa, bullo da matakan neman ciyar da nahiyar gaba ta hanyar warware wasu daga cikin manyan matsalolin dake damunta, tamkar kafa damba ne ga kokarin da ake na aiwatar da ajandar raya nahiyar daga nan da shekara ta 2063.

Taken taron AU na bana dai shi ne "Yaki da cin hanci: hanya mafi dacewa ta farfado da nahiyar Afirka" (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China