in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IOC ta amince wani rukuni na 'yan wasan kasar Rasha su shiga gasar wasannin Olympic ta PyeongChang
2018-01-25 15:00:11 cri

Kwamitin kasa da kasa dake shirya gasar wasannin Olympic ko IOC a takaice, ta wanke wani rukuni na 'yan wasa da yanzu haka ke da damar zuwa birnin PyeongChang na kasar koriya ta arewa, inda za a gudanar da gasar Olympic ta lokacin hunturu ta bana.

IOC dai ta shafe makwanni tana tantance 'yan wasan daya bayan daya, gabanin ba su izinin zuwa gasar ta PyeongChang daga kasar ta Rasha. An ce za a baiwa 'yan wasan takardun gayyatar halartar gasar a ranar 27 ga watan nan a PyeongChang, kafin a wallafa sunayen ilahirin 'yan wasan da aka gayyata zuwa gasar.

Da fari dai an fara tantance 'yan wasa 500 ne daga kasar ta Rasha, kafin kwamitin ya maida adadin zuwa 111. Kwamitin na IOC ya ce za a baiwa ragowar 'yan wasan damar shiga a dama da su, bayan karasa tantance su, ko yayin da suka karasa cika dukkanin ka'idojin da ake bukata.

Kwamitin na IOC ya ce kaso 80 bisa dari na 'yan wasan da aka tantance sabbi ne, wadanda ba su halarci gasar Olympic ta lokacin sanyi a Sochi a shekarar 2014 ba, don haka ana iya cewa 'yan wasan sabbin jinni ne a kasar ta Rasha.

A daya bangaren kuma, kwamitin zai baiwa kwamitin dake kula da gasar Olympic na kasar Rasha wanda aka dakatar, damar gabatar da 'yan wasa da za su cike guraben wadanda ba su cancanci shiga gasar ta PyeongChang ba. Don haka ya zuwa yanzu, ba za a iya tabbatar da cikakken adadin 'yan wasan da za su shiga gasar ta koriya ta kudu daga Rasha ba.

A farkon watan Disambar da ya gabata, IOC ta yanke shawarar hana dukkanin 'yan wasan Rasha shiga gasar ta PyeongChang, bayan da binciken hukumar na sama da watanni 17 ya tabbatar da almundahana, da shan kwayoyin kara kuzari tsakanin 'yan wasan kasar, wadanda suka shiga gasar birnin Sochi a shekarar 2014. Baya ga sauran hukumomi, da sauran masu ruwa da tsaki na kasar da aka tabbatar sun taimakawa 'yan wasan wajen karya ka'idojin gasar.

To sai dai kuma bayan dage wannan haramci, an ce yanzu haka 'yan wasan kasar ta Rasha, za su shiga gasannin PyeongChang da riguna masu sunan kasar su amma da tutar Olympic, kuma za a rika yin take ne na Olympic, a duk lokacin da ake gabatar da su a rukunin wasannin da za su shiga.

A wani ci gaban kuma, ministan wasanni na Rasha Pavel Kolobkov, ya yi Allah wadai da matakin na kwamitin IOC, yana mai bayyana shi da cewa yana cike da rudani.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China