in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta fara aiwatar da dokar biyan haraji kan kare muhalli
2018-02-01 12:56:03 cri
Tun daga ranar 1 ga watan Janairun bana, kasar Sin ta fara aiwatar da dokar haraji kan kare muhalli, dokar haraji ta farko da kasar ta bullo da ita ta fuskar kare muhallin halittunta. Bisa wannan doka, gwamnati za ta ci tarar kamfanonin da suke fitar da abubuwa masu gurbata iska da ruwa da karar injuna masu damun mutane.

Aiwatar da wannan doka na shaida cewa, kasar Sin ta kawo karshen tsarin karbar kudade kan aikace-aikacen dake gurbata muhalli, wanda aka shafe tsawon shekaru kusan arba'in ana amfani da shi.

Bayanai na nuna cewa, matakan da za'a bi domin tattara haraji sun hada da, na farko gwamnatin lardi za ta bullo da matakan biyan haraji, daga bisani, ta gabatar da su ga majalisar dokokin larduna don samun amincewa, haka kuma za ta gabatar da su ga majalisar dokokin kasa gami da majalisar gudanarwa ta kasar Sin don su tantance. Wata muhimmiyar ka'ida ita ce, idan kamfanoni suka fitar da abubuwa masu gurbata muhalli masu dimbin yawa, za su biya haraji mai yawa. Amma idan suka fitar da abubuwa kalilan, ba za su biya haraji mai yawa ba. Alal misali, idan yawan abubuwa masu gurbata muhalli da wani kamfani ya fitar ya yi kasa da kashi 50 bisa dari na ma'auni harajin, to za'a rage rabin harajin da zai biya. Idan yawan abubuwa masu gurbata muhalli da kamfanin ya fitar ya yi kasa da kashi 30 bisa dari, to zai biya harajin kashi 75 bisa dari.

Nan da shekara daya ko biyu masu zuwa da fara aiwatar da wannan doka, za ta yi tasiri ga tattalin arzikin kasar Sin, musamman masana'antun da suke gurbata muhalli. Ya zama dole kamfanoni su yi taka-tsantsan, musamman kamfanonin dake fitar da abubuwa masu gurbata iska da ruwa da karar injuna masu damun mutane da sauransu. Wannan mataki ya tilasta wa kamfanonin gaggauta yin kwaskwarima ga ayyukansu, da kara mai da hankali kan ayyukan kare muhalli. (Ahmed, Saminu, Ibrahim/ Sanusi Chen)


Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China