in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattaunawar Koriya ta arewa da makwabciyarta ta kudu
2018-01-21 10:14:35 cri

A kwanakin baya ne, kasashen Koriya ta arewa da takwararta ta kudu, suka bude kafar tattaunawa tsakanin manyan jami'an sassan biyu a kauyen Panmunjom dake tsakanin kasashen biyu, matakin da kasar Sin da sauran kasashen duniya suka yi na'am da shi matuka.

A yayin wannan tattaunawa ce kasar Koriya ta Arewa ta amince ta tura tawagarta zuwa gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu da za a yi a birnin PyeongChang na Koriya ta kudu a watan Faburairu mai zuwa. Bayan wannan ganawa, Koriya ta Kudu ta sake yin yatin tattaunawa da makwabciyar Koriya ta Arewa a fannin soja.

Wannan matakin ya zo ne kwana guda, bayan da Koriya ta kudu ta bayyana shawarar gudanar da taron manyan jami'ai na kasa da kasa, domin tattauna batun samarwa tawagar jami'an damar zuwa Koriya ta kudu.

Kasar Sin tana goyon bayan inganta dangantakar sassan biyu, da kaucewa ruwa wutar rikici, da kawar da makaman nukiliya a zirin Koriya. Har ila yau Sin tana fatan sassan biyu za su yi amfani da wannan dama wajen cimma buri daya da zai amfane su.

Masu sharhi na maraba da wannan mataki wanda suka ce zai kai ga samar da zaman lafiya tsakanin sassan biyu da ma shiyyar baki daya, duk da rashin fahimtar da a kai ta fuskanta tsakanin wasu kasashen shiyyar da kuma Amurka a daya bangaren, game da shirin Koriya ta Arewa na kera makamai masu linzami. Sai dai har kullum kasar Sin tana kira ne a hau teburin tattaunawa don kawo karshen wannan takaddama. (Saminu, Ibrahim /Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China