in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dan wasan gaban Brazil Souza ya koma Sao Paulo
2018-01-10 16:03:03 cri
Dan wasan gaban kungiyar kwallon kafar kasar Brazil Diego Souza ya koma kulaf din Sao Paulo daga tsohuwar kungiyar sa ta Recife. Recife dai na rike da kofin zakarun kulaflikan kasar ta Brazil har karo 6.

Souza mai shekaru 32 da haihuwa, ya sanya hannu kan kwantiragin shekaru 2, da dama ta cike shekara ta 3 a Sao Paulo, kan kudi har damar Amurka miliyan 3.6. Souza ya ciwa Recife kwallaye 57 a wasanni 173 da ya buga bayan da ya koma can daga Fluminense a shekarar 2016.

Shafin yanar gizo na kungiyar ta Recife ya bayyana cewa, nan gaba cikin 'yan kwanaki masu zuwa za a yi wa dan wasan gwaje gwajen lafiya kafin shigar da shi cikin jerin 'yan wasan kungiyar.

Dan wasan ya kuma taba taka leda a Benfica, baya ga kungiyar kasar sa da ya takawa leda a karo 7, an kuma martaba shi cikin manyan 'yan wasan kungiyar, bayan da ya ciwa Brazil din wata kwallo da aka ce ita ce mafiya sauri a tarihin kungiyar. Ya ciwa Brazil kwallon ne cikin watan Yuni, dakika 11 da take wasa tsakanin kasar Brazil din da Australia, wasan da aka buga a Melbourne, aka kuma tashi Brazil din na da kwallaye 4 Australia na nema.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China