Haka kuma, yace, a halin yanzu, kasar Amurka tana daukar matakan diflomasiyya da na tattalin arziki na kasa da kasa domin warware batun nukiliyar kasar Koriya ta Arewa. A watan Janairu mai zuwa ne sakatare Rex Tillerson wanda ke kula da harkokin wajen kasar Amurka, zai gana da wasu wakilan kasashen duniya kan wannan batu. Lamarin ya nuna cewa, a ganin kasar Amurka, hanyar diflomasiyya ce mafi dacewa wajen warware batun nukiliyar kasar Koriya ta Arewa. (Maryam)