in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Habasha: An kafa majalissar bunkasa sashen gine gine
2017-12-26 09:18:14 cri

Mahukunta a kasar Habasha, su kafa wata sabuwar majalissa da aka dorawa alhakin bunkasa sashen gine ginen kasar, a wani mataki na daga matsayin sashen wanda yanzu haka ke samun karin tagomashi.

Majalissar wadda firaministan kasar Hailemariam Desalegn zai jagoranta, za ta kunshi mambobi daga ma'aikatun gwamnati, da masu ruwa da tsaki daga tsagin gwamnati da masu zaman kan su na kamfanonin gine gine, da 'yan kwangila, da masu rike da mukamin magajin gari, da wakilan kungiyoyin kwararru a fannin.

Da take karin haske yayin bikin kaddamar da majalissar a jiya Litinin, ministar ma'aikatar gine gine ta kasar Aisha Mohammed, ta ce hakan zai share fagen samar da babban ci gaba, ta hanyar samar da sabbin shawarwari, da kirkiro manufofi, tare da gabatar da dabaru da suka jibanci bunkasa sashen na gine gine.

Yanzu haka dai sashen gine gine a kasar ta Habasha na samun ci gaba cikin sauri, inda aka hahikance cewa, yana samar da kaso 9 bisa dari na daukacin GDP kasar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China