Wata sanarwar gwamnatin kasar ta bayyana cewa, jami'an sun kunshi ko dai 'yan kungiyoyin ta'adda, ko kuma mambobin kungiyoyin dake yiwa tsaron kasar kafar ungulu. An kuma kore su daga aikin ne bisa tanajin wata doka ta soja. A hannu guda kuma, an maida wasu jami'ai su 115 bakin aikin su, bayan korar da aka yi musu a baya.
Mahukuntan Turkiyyar dai na ci gaba da gudanar da bincike, tare da daukar matakan hukunta wadanda aka samu da hannu a yunkurin juyin mulkin soji da bai yi nasara ba na watan Yulin da ya gabata. Lamarin da kuma ya sabbaba kisan mutane 250.
Kawo yanzu dai an kori ko dakatar da jami'ai sama da 150,000 daga aiki, kana ana tsare da wasu 55,000, bisa batun juyin mulkin da mahukuntan Turkiyyan ke alakantawa da malamin addinin nan Fethullah Gulen, wanda yanzu haka ke gudun hijira a Amurka.