A game da wannan, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Hua Chunying a taron manema labarai da aka kira yau Jumma'a, ta bayyana cewa, labarin ya jawo hankalin kasar Sin, kuma kullum kasar ta Sin na adawa da duk wani matakin da ka iya iya lahanta lafiyar fararen hula, da kuma tsananta rikici.
Kakakin ta ce, yau sama da shekaru biyu ke nan da ake fama da rikicin soja a kasar Yemen, kuma matakin gaggawa da ake bukata shi ne sassa daban daban su cimma wani shiri da zai kai ga warware matsalar ta hanyar yin shawarwari da juna.(Lubabatu)