in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron kare hakkin bil-Adama tsakanin kasashe masu tasowa da ya gudana a kasar Sin
2017-12-29 06:35:51 cri

A kwanan baya ne, aka shirya taron dandalin tattaunawa game da kare hakkin bil Adam a tsakanin kasashe maso tasowa wato SSHRF a takaice, karo na farko, da aka gudanar taron a nan birnin Beijing na kasar Sin.

Taron ya samu halartar wakilai fiye da 300 daga kasashe daban daban na duniya, kwararrun masana, da kuma jami'an kungiyoyin kasa da kasa kimanin 70 wadanda suka gabatar da kasidu tare da bayyana ra'ayoyinsu game da muhimmancin ba da fifiko ga kare batun hakkin dan adam.

Masana da dama sun bayyana irin alfanun da kasashen Afrika za su samu game da wannan taro wanda ma'aikatar watsa labarai da hadin gwiwar ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin suka shirya.

A cikin sakonsa na fatan alheri da ya aike don murnar bude dandalin, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya yi kira da a mutunta muradun kasashe masu tasowa a fannin kare hakkin bil-Adama.

Shugaba Xi, ya ce wajibi ne, a yayata batun kare hakkin dan-Adam bisa la'akari da yanayi da bukatun al'ummomin kasashen duniya musamman a kokarin wanzar da zaman lafiya, samar da ababen more rayuwa da kuma gina kyakkyawar makoma ga bil adama a nan gaba.

Har ila, mahalarta taron na kwanaki biyu sun tattauna ci gaban ayyukan kare hakkin dan Adam na kasashe masu tasowa da na duniya, daga bisani kuma aka zartas da sanarwar Beijing.

Cikin sanarwar, an bayyana cewa, hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa, wata muhimmiyar hanya ce ta ci gaban kasashen, da kuma aikin kare hakkin dan Adam na sassan. Sanarwar ta nuna cewa, ya kamata kasashen su hada kansu a wannan fanni bisa ka'idojin kwazo tare, da sauke nauyin da ke wuyansu, da taimakawa juna don cimma nasara gaba daya, ta yadda za a iya ba da tabbaci sosai ga aikin kare hakkin dan Adam.

Bugu da kari, sanarwar ta bukaci sassan kasa da kasa, su kara nuna goyon baya ga saurin bunkasuwar kasashe masu tasowa, da kyautata aikinsu a fannin ba da tabbaci ga hakkin dan Adam, bisa ka'idojin samun daidaito, da kai zuciya nesa, da samar da moriya ga jama'a, kana da samun dauwamammen ci gaba.

A jawabinsa yayin taron, ministan harkokin wajen kasar Sin Mr. Wang Yi, ya ce tun bayan kafuwar Jamhuriyar jama'ar Sin, kasar Sin ta samu gaggarumar nasara a fannin kare hakkin bil Adam, a karkashin jagorancin jam'iyyar Kwaminis ta kasar mai sigar musamman na kasar Sin. (Ahmed, Ibrahim/ Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China