A wannan rana kuma, babban kwamandan cibiyar bada jagoranci kan hadin gwiwar Iraki Abdul Amir Yarallah, ya fidda wata sanarwa inda ya bayyana cewa, a ranar 9 ga wata sojojin gwamnatin kasar da sojojin kungiyar mabiya Shi'a sun 'yantar da wani yankin dake tsakanin lardin Al-Anbar da lardin Ninewa, lamarin da ya nuna cewa, sun karbi ikon yankin iyakar dake tsakanin kasar Iraki da kasar Syria baki daya.
Mr. Yarallah ya kara da cewa, ya zuwa yanzu sojojin gwamnatin kasar Iraki sun 'yantar da dukkan wuraren da suka taba zama karkashin ikon kungiyar masu da'awar kafa daular musulunci ta IS. (Maryam)