Jean Pierre Lacroix, ya ce sun damu kwarai da tabarbarewar tsaro dake kara kamari a Sudan ta kudu. Ya ce yayin da aka shiga lokacin hunturu, akwai yiwuwar rikicin dake tsakanin sojoji da kuma wanda ke kabilun kasar ya ta'azzzara.
Ya kuma bukaci kwamitin sulhun ya kara kaimi wajen ganin an sulhunta rikicin a siyasance.
Jim kadan bayan samun 'yancin kai a shekarar 2011 ne, Sudan ta Kudu ta fantsama cikin yakin basasa, inda aka yi kiyasin mutane 300,000 sun mutu tun daga karshen shekarar 2013. Sannan, sama da mutane miliyan 1.5 ne suka tsere zuwa kasashen makwabta, galibi kuma na gudun hijira a cikin kasar. (Fa'iza Mustapha)