Jakadan kasar Sin dake kasar ta Zimbabwe Huang Ping wanda ya bayyana hakan a jiya Laraba yayin bikin sanya hannu kan yarjejeniyar ba da rancen, ya ce za a yi amfani da kudaden wajen aikin fafadawa da kuma daga matsayin filin jiragen saman kasar, da gina sabon zauren majalisar dokokin kasar, da kashi na biyu na aikin gina cibiyar harkokin na'ura mai kwakwalwa ta zamani, cibiyar harkokin na'ura mai kwakwala mafi sauri ta uku a nahiyar Afirka.
Jakada Huang Ping ya ce, kasar Sin tana farin cikin rantawa kasar ta Zimbabwe wadannan kudade, kana za ta ci gaba da taimaka mata a kokarin da kasar ke yi na farfado da tattalin arziki da jin dadin rayuwar al'ummominta.
A nasa jawabi ministan kudi na kasar Zimbabwe Patrick Chinamasa, ya ce, taimakon kudaden da kasar Sin ta baiwa kasarsa alama ce da ke nuna dadadden zumuncin dake tsakanin kasashen biyu.
Ya ce, gina kayayyakin more rayuwar, za su taimaka matuka wajen samar da guraben ayyukan yi ga mazauna wurin, baya ga bunkasa harkokinsu na kasuwanci.
Yarjeniyoyin taimakon kudin su ne na farko da gwamnatin shugaba Emmerson Mnangagwa ta sanyawa hannu tun bayan kama aiki, kuma suna daga cikin alkawuran da sassan biyu suka cimma game da wasu ayyuka yayin ziyarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai kasar ta Zimbabwe a shekarar 2015.(Ibrahim)