in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rawar da abinci ke takawa wajen kawar da talauci
2017-10-26 08:28:10 cri

Ana bikin ranar samar da abinci ta duniya ce a ranar 16 ga watan Oktoban kowace shekara don karrama ranar da aka kafa hukumar samar da abinci da aikin gona ta MDD (FAO) da aka yi a shekara ta 1945.

Kasashe mambobin hukumar FAO ce suka kebe wannan rana a babban taron hukumar karo na 20 da ya gudana a watan Nuwamban shekarar 1945.

Tun wancan lokaci ne, yayin da ake bikin wannan rana, ake bullo da taken da zai kasance a shekarar, misali yakar yunwa don rage talauci ko zuba jari a bangaren aikin gona don kara samar da abinci da sauransu. Taken ranar bikin na bana, shi ne canja makomar 'yan gudun hijira, zuba jari a fannin samar da abinci da raya yankunan karkara.

Wani rahoto da shirin samar da abinci na duniya (WFP) ya fitar, ya nuna cewa, akwai mutane kimanin sama da miliyan 800 a duniya da ke fama da matsalar yunwa, ko da yake matsalar ta ragu idan aka kwatanta da shekarun baya.

Bugu da kari, masana sun bayyana cewa, akwai gibi sosai a tsakanin burin rage rabin yawan mutanen da ke fama da yunwa a shekara ta 2015 da MDD ta gabatar, kana akwai rahotannin da ke nuna cewa, saboda karuwar yawan jama'a a duniya, yawan bukatar abinci a duniya nan da shekara ta 2050 za ta karu da kashi 60 cikin 100 bisa na yanzu.

Wannan ne ya sa masana ke ganin cewa, akwai bukatar mahukunta, kungiyoyin kasa da kasa da sauran jama'a da su tashi tsaye wajen shata manufofi da shirye-shirye a kokarin ganin an warware matsalar abinci da ake fuskanta a duniya. (Ahmed, Fa'iza, Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China