in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ranar zaman lafiya ta duniya
2017-09-28 14:46:40 cri

A ranar 21 ga watan Satumban wannan shekara ta 2017 ne aka yi bikin ranar zaman lafiya ta duniya na bana. An dai fara bikin wannan rana ce a shekara 1982. A shekarar 1981 ne babban taron MDD ya yanke kudurin gudanar da bikin a wancan shekara.

Da farko dai an shirya bude babban taron shekara-shekara na MDD ne a ranar Talata ta uku na watan Satumba, sai aka canja ranar a shekarar 2001 zuwa ranar 21 ga watan Satumba.

Taken bikin ranar zaman lafiya na bana, shi ne hadin gwiwa don samar da zaman lafiya: mutunta juna, kare da kuma martaba kowa da kowa".

A wannan karo, an mayar da hankali ne kan ilimantar da jama'a a duk fadin duniya game da nuna goyon baya ga 'yan gudun hijira da bakin haure. Bugu da kari, bikin na bana ya nuna cewa, matasa suna da rawar takawa, misali taimakawa 'yan gudun hijira da bakin haure a yankunansu da wadanda za su iya gamuwa da su ko a azuzuwa ko makwabtansu da dai sauransu.

Masana na ganin cewa, muddin ana bukatar samun duniya mai zaman lafiya da wadata, wajibi ne jama'a su rika mutuntawa tare da taimakawa juna a lokacin da bukatar hakan ta taso. (Saminu, Fa'iza, Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China